Tsakure
Manufar wannan
maƙala ita ce
nazartar al’adun Hausawa a duniyar intanet ta yau. An ɗora aikin a kan Bahaushen
ra’i na Zamani Riga. Kadadar binciken ta taƙaita ga al’adun Hausawa da duniyar intanet. Tussan
bayanai na farko da aka yi amfani da su sun kasance kafafen intaent kai tsaye.
Majiya ta biyu kuwa ta kasance ayyukan da suka gabata waɗanda suke da alaƙa da wannan bincike. Sakamakon binciken ya nuna
cewa, tuni Hausa ta kama hanyar samun gagarumin gindin zama a duniyar intanet. Al’adun Hausawa
daban-daban na bayyana yayin da aka neme su ta hanyar injunan biɗar bayanai na kan intanet. Ƙalubalen da ake fuskanta
a wannan haujin sun haɗa da ƙarancin masana masu
jagorantar lamuran kafafen intanet na Hausa, da kuma rashin ingancin bayanan da
ake ɗorawa a kan kafafen. Daga ƙarshe, binciken
ya nuna wajibcin ƙara himma ga masana da manazarta harshe da adabi da kuma al’adun Hausawa
wajen sanya rigar zamani da samar da kyakkyawan wakilci a duniyar intanet.
Fitilun Kalmomi: Hausa, Hausawa, Al’adu, Intanet, Duniyar Intanet
DOI: 10.36349/zamijoh.2023.v02i03.010
author/Abu-Ubaida SANI & Adamu Rabi’u BAKURA
journal/Zamfara IJOH Vol. 2, Issue 3