Tsakure
Sauyi a ilimin ƙirar kalma batu ne mai matuƙar muhimmanci. Haka kuma, babban guzuri ne na
bayanin fasalin ƙirar kalmomi a harshe. A Hausa, fitattun ayyukan da suka yi bayani a kan
sauyi, akwai Malumfashi (1986) wanda ya yi a kan sauyi na ƙirar kalma, sai Yakasai (2006) wanda ya mayar da
hankali a kan sauyin zati da na nahawu a muhallin ninki a Hausa. Shi kuwa Sani
(2011), ya yi bayani ne a kan wasu daga cikin sauye-sauyen da akan samu ta
fuskar tsarin sauti. Wannan ya nuna salon binciken da aka yi wa sauyi a ilimin ƙirar kalma na zaman ‘yan marina ne, domin kuwa, kowanne
da inda ya sa gaba, watau ba a haɗa su wuri ɗaya balle ma a fito da kyawun
da yake cikin wannan sauyi. A taƙaice dai, wannan maƙala ta ƙudurci tattaro waɗannan sauye-sauyen tare da yin bayanin kowanensu da
kuma yadda yake aukuwa a tsakanin kalmomin Hausa saboda ganin irin muhimmiyar
rawar da suke takawa wajen bayanin abin da ya shafi ginin kalmomi. Waɗannan sauye-sauyen su ne: Sauyi na tsarin sauti;
kamar a kalmomin gidaa da gidàajee da sauyi na ƙirar kalma; kamar a ràagoo da tunkìyaa da sauyi na
zatin kalma; kamar a laalàataa da magoorii da sauyi na al’umma; kamar a kalmar kyâutaa
a al’ummar Sakkwato da Kano da kuma sauyi na nahawu; kamar a tàakàa lumui da tàakàlmii
ko saura yà yii da sauràyii. Muƙalar ta ƙunshi gabatarwa sai bayani a kan ilimin ƙirar kalma da kuma bayani a kan sauye-sauyen da akan
samu a ƙirar kalmomin Hausa.
Fitilun Kalmomi: Ƙirar Kalma, Rikiɗa, Hausa
DOI: 10.36349/zamijoh.2023.v02i03.001
author/Dr. Isah A. Muhammad & Abdullahi Bashir
journal/Zamfara IJOH Vol. 2, Issue 3