Kalmomin Masu Sayar da Man Fetur da Baƙin Mai a Garin Sakkwato

    Tsakure

    Wannan takarda ta yi nazarin kalmomin rukunin masu sayar da man fetur da baƙin mai a cikin garin Sakkwato. Manufar ita ce, zaƙulo yadda wannan rukunin ‘yan kasuwa suke sarrafa harshen Hausa, ta hanyar fito da ma’anonin kalmomin da suke amfani da su a zantukansu na yau da kullum. An taƙaita wannan bincike a kan nazarin kalmomi ne kawai, ba tare da nazarin sassan jumla ko jumlolin wannan rukunin ‘yan kasuwa ba. An gabatar da hasashe guda biyu (2), waɗanda aka gwada su ta hanyar gudanar da lura ta kai-tsaye da hira ko tattaunawa da masu harkar sayar da man fetur da baƙin mai a wuraren kasuwancinsu. An tattaro wasu lafuzzan da suke amfani da su domin tabbatar da samuwar wannan Hausar dalilin zamantakewa da sauran ma’amalolin a wuraren kasuwancinsu. Binciken ya gano cewa ‘yan kasuwar suna amfani da wasu ma’anoni na musamman waɗanda suka sha bamban da yadda sauran jama’a suka san su a Hausar yau da kullum. Binciken kuma ya gano cewa ma’anonin da suke amfani da su sun samu ne daga faɗaɗa ma’ana da ƙirƙira da kuma sarrafa kalmomin aro.

    Fitilun Kalmomi: Kalmomi, Man Fetur, Baƙin Mai

    DOI: 10.36349/zamijoh.2025.v04i01.010

    Download the article:

    author/Dr. Muhammad Mustapha Umar

    journal/Zamfara IJOH Vol. 4, Issue 1

    Pages