Kinin Ma’ana a Wasu Waƙoƙi Ummaru Bagobiri: Nazari Ta Fuskar Muhallin Magana

    Tsakure

    Wannan takarda ta yi bayanin yadda Ummaru Bagobiri ke amfani da kalmomi da suke da bambancin ma’ana a matsayin kalmomi masu kinin ma’ana wajen gina ɗiyan waƙoƙinsa. Irin waɗannan kalmomi kan samu bambanci dangane da ma’anonin da suke ɗauke da su, amma Ummaru Bagobiri na amfani da hikimarsa wajen amfani da su cikin jumla a matsyin kalmomi masu kinin ma’ana. Hanyoyin da aka bi wajen tattaro bayanai dangane da wannan takarda kuwa, sun haɗa da sauraren waƙoƙin Ummaru Bagobiri da ganawa da masana da suke da alaƙa da ɓangaren ilimin kimiyyar harsuna. An kuma karanta ayyukan da masana suka wallafa dangane da waɗannan ɓangarori na ilimin kimiyyar harsuna, musamman waɗanda suka shafi ilimin ma’ana. An kuma yi amfani da hanyar hira da ma’abota saurarren waƙoƙin Ummaru Bagobiri don jin irin ma’anonin da kalmomin ke ɗauke da su. Don ganin an sami madogara dangane da bayanan da aka yi cikin wannan takarda, an ɗora wannan bincike ne a kan ra’in Speber da Wilson, 1995, waɗanda suka samar da ra’in dangane da muhallin magana a bigeren alaƙa. Binciken ya gano cewa muhallin magana na taka rawa sosai wajen fayyace ma’anar irin waɗannan jimloli. Har wa yau, binciken ya gano cewa Ummaru Bagobiri na amfani da hikimarsa wajen amfani da kalmomi masu mabambanciyar ma’ana a matsayin kalmomi kalmomi masu kinin ma’ana wajen ginin ɗiyan waƙoƙinsa.

    Fitilun Kalmomi: Waƙƙoƙi, Ma’ana, Kalmomi, Kinin Ma’ana, Waƙoƙi.

    DOI: 10.36349/zamijoh.2025.v04i01.009

    Download the article:

    author/Bello, M.Z. & Ibrahim, S.

    journal/Zamfara IJOH Vol. 4, Issue 1

    Pages