Yanayin Korona A Idon Al’umma: Tsokaci Daga Bakin Marubuta Waƙoƙin Hausa

    Tsakure: Taken wannan maƙalar shi ne “Yanayin Korona a Idon Al’umma: Tsokaci Daga Bakin Marubuta Waƙoƙin Hausa”. An shirya wannan maƙalar ne domin duba yadda wasu marubuta waƙoƙin Hausa suka fito da yadda al’umma suke kallon annobar Korona a cikin waƙoƙinsu. Annobar Korona sabuwar cuta ce da Hausawa ba su san ta ba kafin watan Disamba 2019, inda ta bayyana a birnin Wuhan na ƙasar Sin, ta yaɗu a sassan duniya duka. Kasancewar waƙa wani nau’in adabi ne mai tafiya daidai da zamani ya sa aka samu wanzuwar wasu rubutattun waƙoƙin Hausa na Korona. Hanyoyin da aka bi wajen gudanar da binciken sun haɗa da tattaro rubutattun waƙoƙin Hausa da aka yi a kan annobar Korona, aka tsettsefe su da karance-karance a ɗakunan karatu na jami’o’i da tattaunawa da masana a harkar adabi da wasu marubuta waƙoƙin da kuma likitoci. Ra’in Tarihanci (Historicism Theory) ne ya jagoranci binciken domin samun ingantaccen sakamako. A ƙarshe maƙalar ta fito da gudummuwar da marubuta waƙoƙin Hausa suka bayar wajen bayyana yadda al’umma suke kallon annobar Korona kama daga Sarakuna da malamai da talakawa da kuma hukuma..

    Fitilun Kalmomi: Annoba, Korona, Al’umma, Marubuta da Waƙoƙin Hausa

    DOI: 10.36349/zamijoh.2026.v04i02.004

    Download the article:

    author/Bashir A. S., Bunza U. A. & Abba M. M.

    journal/Zamfara IJOH Vol. 4, Issue 2

    Pages